Acts 1

1Littafin da na rubuta da farko, Tiyofilos, ya fadi abubuwan da Yesu ya fara yi ya kuma koyar, 2har zuwa ranar da aka karbe shi zuwa sama. Wannan kuwa bayan da ya ba da umarni ga zababbun manzanninsa ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 3Bayan ya sha wahala, ya bayyana kan sa da rai a garesu, da alamu da dama masu gamsarwa. Kwana arba’in ya baiyana kansa a garesu yana yi masu magana game da mulkin Allah.

4Yayin da yana zaune tare da su ya basu umarni cewa kada su bar Urushalima, amma su jira alkawarin Uban, wanda ya ce, ‘’Kun ji daga gare ni, 5cewa Yahaya babu shakka ya yi baftisma da ruwa, amma ku za a yi maku baftisma da Ruhu Mai Tsarki nan da kwanaki kadan.‘’

6Sa’adda suna tare suka tambaye shi, ‘’Ubangiji, a wannan lokaci ne za ka maido da mulki ga Isra’ila?” 7Ya ce masu, ‘’Ba naku bane ku san lokaci ko sa’a wanda Uba ya shirya ta wurin ikonsa. 8Amma za ku karbi iko, idan Ruhu Mai Tsarki ya zo bisanku, sa’annan za ku zama shaidu na cikin Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, har ya zuwa karshen duniya.”

9Lokacin da Ubangiji Yesu ya fadi wadannan abubuwa, yayin da suna kallon sama, sai aka dauke shi zuwa sama, kuma girgije ya boye shi daga idanunsu. 10Da suka dinga kallon sama yayin da ya tafi, nan da nan, mazaje biyu suka tsaya a gabansu cikin fararen tufafi. 11Suka ce, ‘’Ku mazajen Galili me yasa ku ke tsaye a nan kuna kallon sama? Wannan Yesu wanda ya hau zuwa sama zai dawo kamar yadda kuka gan shi yana tafiya zuwa sama.‘’

12Da suka dawo Urushalima daga dutsen Zaitun, wanda ke kusa da Urushalima, tafiyar Asabaci daya ne. 13Da suka iso, sai suka haye zuwa cikin bene inda suke da zama. Sune su Bitrus, Yahaya, Yakubu, Andarawus, Filibus, Toma, Bartalamawus, Matiyu, Yakubu dan Alfa, Siman mai tsattsauran ra’ayi, kuma da Yahuza dan Yakubu. 14Dukansu kuwa suka hada kai gaba daya, yayin da suka ci gaba da naciya cikin addu’a. Tare da su kuma akwai mata, Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma ‘yan’uwansa.

15A cikin wadannan kwanaki Bitrus ya tashi tsaye a tsakiyar ‘yan’uwa, kimanin mutane dari da ashirin, ya ce, 16‘’ ‘Yan’uwa, akwai bukatar Nassi ya cika, wanda Ruhu Mai Tsarki ya fada a baya ta bakin Dauda game da Yahuza, wanda ya jagoranci wadanda suka kama Yesu

17Domin yana daya daga cikinmu kuma ya karbi rabonsa na ladan wannan hidima,” 18(Wannan mutum fa ya sai wa kansa fili da cinikin da ya yi na muguntarsa, kuma a nan ya fado da ka, cikinsa ya fashe, hanjinsa suka zubo waje. 19Duka mazaunan Urushalima suka ji wannan, saboda haka suka kira wannan fili da harshensu “Akeldama‘’ wato, “Filin Jini.”)

20“Domin an rubuta a littafin Zabura, ‘Bari filinsa ya zama kufai, kada a bar kowa ya zauna wurin,’kuma, ‘Bari wani ya dauki matsayinsa na shugabanci.’

21Saboda haka ya zama dole, daya daga cikin wadanda suke tare da mu tun lokacin da Ubangiji Yesu yana shiga da fita, a tsakaninmu, 22farawa daga baftismar yahaya har zuwa ranar da aka dauke shi daga wurinmu zuwa sama, ya zama daya daga cikin mu wurin shaidar tashinsa.” 23Suka gabatar da mutum biyu, Yusufu wanda ake kira Barsabbas, wanda kuma aka yiwa suna Justus, da kuma Matayas.

24Su ka yi addu’a suka ce, ‘’Ubangiji, kai ka san zuciyar dukan mutane, ka bayyana mana wanda ka zaba cikin su biyun nan 25Domin ya dauki gurbin da kuma manzancin daga inda Yahuza ya kauce zuwa nashi waje‘’ suka jefa kuri’a a kansu; zabe ya fada kan Matayas kuma suka lissafta shi tare da manzanni sha dayan.

26

Copyright information for HauULB